Harin jirgin yaki a Tudun Biri
Harin jirgin yaki a Tudun Biri | ||||
---|---|---|---|---|
airstrike (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Kwanan wata | 3 Disamba 2023 | |||
Perpetrator (en) | Nigerian Air Force (en) | |||
Wuri | ||||
|
Hare-haren jirgin yaki na Sojan Najeriya a Tudun Biri, An samu faruwar, hare-haren bom da wani jirgin yaki na Sojan Najeriya maras matuki a kauyen Tudun biri. Harin ya faru ne da yammacin ranar, 3 ga watan Disamba, 2023, yayin bikin Mauludi a kauyen dake jihar Kaduna, Najeriya, a wani bangare na ayyukan yaki da ta'addanci. Rundunar sojin Najeriya ta aiwatar da hukuncin kisa, harin da jirgin maras matuki yayi, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da mutane 85, galibinsu mata ne da kananan yara a kauyen Tudun Biri, lamarin da ya haddasa samuwar raunuka da kuma tashin hankali.[1][2][3]
Fage
[gyara sashe | gyara masomin]Tare da hadin gwiwa da kawayen kasashen duniya, ciki harda Amurka da Birtaniya, sojojin Najeriya na da tarihin yin amfani da fasahar maras matuki wajen yaki da ta'addanci. Lamarin da ya faru a Tudun Biri ya nuna irin sarkakiya da kasadar da ke tattare da irin wadannan ayyuka.[4]
Hari
[gyara sashe | gyara masomin]Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da mutuwar fararen hular da ba'a yi niyya ba, inda rahotanni ke nuna adadin wadanda suka mutu ya haura mutane 85. A yayin wani taron tsaro, shugaban addini Sheikh Rabi'u Abdullahi ya bada rahoton mutuwar mutane sama da 50, inda ya jaddada tasirin wadanda suka halarci bikin Mauludi.[5]
Bayan haka
[gyara sashe | gyara masomin]Shugaba Bola Tinubu ya nuna juyayi tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.[6] A cikin wata sanarwa da ya fitar a hukumance, ya bayyana shi a matsayin "abin takaici, damuwa, kuma mai radadi," yana mai jaddada bukatar yin nazari sosai kan al'amuran da suka dabaibaye harin da jirgin mara matuki.
Binciken da ake yi na fuskantar kalubale saboda matsalar tsaro a yankin. Manjo VU Okoro, babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya, ya bayyana cewa, harin da jirgin mara matuki ya kai ga al’umma a lokacin da suke aikin yaki da ta’addanci ne.[7]
Lamarin ya haifar da tunani a kan daidaito tsakanin manufofin tsaron kasa da kuma wajabcin kare rayukan fararen hula. A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Tudun Biri ya zama abin tunatarwa ne kan irin kalubalen da sojojin Najeriya ke fuskanta wajen kare al'ummomi yayin da ake yaki da ta'addanci.[8][9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Muhammad, Garba (2023-12-04). "Civilians killed in Nigerian drone attack in north - officials, witnesses". Reuters (in Turanci). Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "Harin Bama-Bamai Kan Masu Maulidi A Kaduna Ya Fusata 'Yan Najeriya". Arewa Radio (in Turanci). Retrieved 2023-12-05.
- ↑ Sulaiman (2023-12-04). "Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna" (in Turanci). Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "'Dole a hukunta wadanda suka hari ta sama a jihar Kaduna'". BBC News Hausa. 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "Nigeria army drone strike accident kills 85 civilians". The East African (in Turanci). 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "Tinubu ya ce a gudanar da bincike kan harin da ya kashe masu Mauludi a Kaduna". RFI. 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "ACF seeks investigation of military drone attack on Tudun Biri community - SolaceBase" (in Turanci). 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "Military Drone Attack Kills 85 People in Nigerian Village". Voice of America (in Turanci). 2023-12-05. Retrieved 2023-12-05.
- ↑ "Nigerian military drone attack kills 85 civilians in error". Al Jazeera (in Turanci). Retrieved 2023-12-05.